<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>98</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Da suna wanda ba mai fi a dukan zamanai,
 Yesu ne, marar zunubi, Ɗan Allah, shi kaɗai.

[V2]
 2) Allah ya sanya sunan nan kan sauran sunaye.
 Mu yabe shi da rairawa, mu gusa gun kursiyi.

[V3]
 3) Mai kayan tulin laifofi shi faɗi sunan nan,
 A cikinsa ga gafara, ba shakka, ko kaɗan.

[V4]
 4) Sunan, idan ka faɗe shi, an ji addu'arka.
 Laifinka ba ya dubawa, sai jinin giciyensa.</lyrics>
<title>Da Suna Wanda Ba Mai Fi A Dukan Zamanai LW98</title>
</song>